Shugabannin kasashen Faransa, Jamus, Italiya, Spaniya, Chadi, Nijer, Libya da sauran kasashe da kuma wakilan kungiyar EU ne suka halarci taron. Bayan taron shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana wa manema labaru cewa, kamata ya yi bangarori daban daban ciki har da kasashen da 'yan gudun hijira suke fitowa da su canja alakar jirgen, kana su dauki matakai tare don tinkarar batun, wannan wani kalubale ne da kungiyar AU da EU ya kamata su fuskanta tare.
Rahotanni na cewa, a yayin taron, an tsai da kudurin kara nuna goyon baya ga Jamhuriyar Nijer da Chadi, da kara sa kaimi ga samar da zaman lafiya a fannin siyasa a kasar Libya. Haka kuma kasashen Faransa da Jamus da Italiya da kuma Spaniya sun yi alkawarin kara yin hadin gwiwar tattalin arziki don kyautata yanayin zaman rayuwar jama'a dake gudun hijira. (Zainab Zhang)