Kamfanin dillancin labarai na kasar Qatar ya ruwaito shugaban hukumar kula da ayyukan AU Moussa Faki Mohammed, na bayyana matsayin Tarayyar dangane da rikicin, inda ya yi kira da a warware shi ta hanyar hawa teburin sulhu da matakan diflomasiyya.
Mataimakin Firaministan Qatar kuma Ministan kula da harkokin Gwamnatin Kasar Ahmed bin Abdullah bin Zaid Al Mahmud, ya yi wa shugaban na hukumar AU bayyani dangane da halin da rikicin ke ciki, ranar Juma'a da ta gabata a birnin Addis Ababa na Ethiopia.
Ya kuma mika godiyar kasarsa game da matsayin da AU ta dauka dangane da batun warware rikicin ta hanyar shiga tattaunawa mai ma'ana tsakanin bangarorin dake rikici, tare da goyon bayan da ta nuna ga yunkurin shiga tsakani da Sarkin Kuwait Sheikh Sabah al-Ahmad al-Jaber ke jagoranta. (Fa'iza Mustapha)