Xi ya bayyana hakan ne jiya Alhamis yayin da yake ganawa da manyan jami'an sojojin kasar a birnin Beijing, fadar mulkin kasar. Xi wanda har ila shi ne babban kwamandan sojojin kasar, ya bukaci sojojin kasar ta Sin da su kasance masu gaskiya da martaba dokokin aikinsu.
Ya kuma bukacin sojojin, da su koya kana su aitawar da ruhin babban taron wakilan JKS karo na 19, su bi turbar gina rundunar soja mai karfi wadda za ta dace da sigar kasar Sin kana su yayata tsarin tsaro da harkar soja na zamani.
Shugaba Xi ya ce akwai bukatar a mayar da hankali wajen yiwa sojojin kasar gyaran fuska ta yadda za su kasance babu kamar su a duniya nan da tsakiyar karni na 21.(Ibrahim)