#JKS19# Xi Jinping: Ya kamata a yi kokarin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama
Xi Jinping ya ce, tun lokacin da aka kaddamar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, ya zuwa yanzu, gaba daya akwai manyan jam'iyyun siyasa 452 daga kasashe 165 wadanda suka aiko da sakwannin taya jam'iyyar murna da fatan alheri game da bude wannan taron guda 855. Daga cikin wadannan sakwanni, akwai guda 814 wadanda shugabannin kasashe, ko kusoshin gwamnatoci, ko kuma manyan jagororin jam'iyyun siyasa da na kungiyoyi suka aiko. Game da hakan, Xi Jinping ya nuna matukar godiya a madadin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.
Xi ya kuma ce, al'ummar kasar Sin za su yi tsayin daka wajen kiyaye yanci da yankunan kasar, da tabbatar da zaman lafiya, gami da neman ci gaban kasa cikin lumana. Kana, za su himmatu tare da ragowar al'ummar kasashen duniya, domin raya duniya mai kyakkyawar makoma ga dukkanin bil'adama, da kuma kara bayar da babbar gudummawa ga aikin shimfida zaman lafiya da neman ci gaba a duniya baki daya. (Murtala Zhang)