in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Syria na shirin kwace tungar mayakan IS ta karshe dake al-Bukamal
2017-10-26 10:02:42 cri

Rahotanni daga Syria na cewa, dakarun gwamnati na kara dannawa zuwa wajen lardin Deir al-Zour dake gabashin kasar Syria a fafatawar da suke da mayakan IS a yankin al-Bukamal, babbar tungar mayakan na IS ta karshe dake kusa da kan iyakar kasar Iraki.

Wata majiyar soja da ta bukaci a sakaye sunanta, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, yanzu haka dakarun Syria na kokarin kwace wani filin mai kafin su nausa har zuwa yankin al-Bukamal, 'yan kwanaki bayan da dakarun gwamnatin suka fatattaki mayakan na IS daga birnin al-Mayadeen, wanda a baya ake dauka a matsayin babban birnin mayakan IS a Deir al-Zour.

Ita ma kungiyar nan dake kula da batun kare hakkin dan-Adam ta kasar Syria, ta bayar da rahoto game da nasarar da sojojin na Syria ke samu a kan mayakan na IS.

A halin da ake ciki, dakarun sa-kai na Hashid Shaabi na kasar Iraki, sun daura damarar kawar da mayakan IS daga yankunan dake hannunsu wadanda ke kan iyakar Tandem na kasar Iraki.

Bayanai na nuna cewa, da wuya a gudanar da taron Geneva game da batun Syria, muddin kungiyoyin 'yan adawar Syria suka gaza gabatar da tawaga guda a wajen taron, daya daga cikin sharuddan da kasar Rasha ta gindaya(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China