in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu shugabannin kasa da kasa da jam'iyyu sun yi aikowa Xi Jinping sakon murnar zama babban sakataren JKS
2017-10-26 09:24:03 cri

Wasu shugabannin kasa da kasa da jam'iyyu sun aika da wasika ko bugo waya domin taya Xi Jinping murnar zama babban sakataren JKS. Shugaban jam'iyyar PNDS-Tarayya kuma ministan harkokin cikin gida na kasar Nijer Mohamed Bazoum ya bayyana cikin wasikar da ya aiko cewa, ya yi imani cewa, a karkashin shugabancin Xi Jinping, jama'ar Sin za su ci gaba da samun nasara wajen cimma burin raya kasar na inganta rayuwar al'ummar Sinawa da cimma manufar "kafa zaman al'umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni a yayin da JKS ta cika shekaru 100 da kafuwa, da kafa kasar Sin mai tsarin gurguzu ta zamani mai wadata, bin tsarin demokuradiya, wayin kai da kuma jituwa nan da shekara 2049, wato yayin bikin cika shekaru 100 da kafa jamhuriyar Jama'ar Sin".

Shi kuma shugaba Paul Biya na Kamaru kana shugaban jam'iyyar R.D.P.C. ya bayyana a cikin wasikarsa cewa, ya yi farin ciki da samun labarin cewa, Xi Jinping ya sake zama babban sakataren JKS. A madadin daukacin 'yayan jam'iyyarsa, shugaba Biya ya taya Xi Jinping murna, tare da fatan zai kara samun nasara a sabon wa'adin aikinsa.

A cikin wasikar da ya aiko, shugaba Jose Mario Vaz na kasar Guinea-Bissau ya ce, a madadin dukkan jama'ar kasar ta Guinea-Bissau, ya taya Xi Jinping murna, tare da fatan jama'ar Sin za su ji dadin zama har abada.

Ban da haka kuma, shugabannin kasashen Rasha, Birtaniya, Faransa, Habasha, Mauritaniya, Ukrain, Iraki, Sham, Japan da dai sauransu da shugabannin jam'iyyu su ma sun aiko da wasika ko buga waya domin taya Xi Jinping murnar zama babban sakataren JKS. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China