in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#JKS19# An ba da sanarwar cikakken zama na farko na kwamitin tsakiya na JKS karo na 19
2017-10-25 12:22:56 cri

A yau Laraba ne agogon kasar Sin, aka gudanar da cikakken zama na farko na kwamitin tsakiya na JKS karo na 19 a birnin Beijing.

Xi Jinping ne ya shugabanci taron, daga bisani kuma ya gabatar da muhimmin jawabi bayan da aka zabe shi a matsayin babban sakataren jam'iyyar.

Haka kuma a yayin taron, an zabi kusoshin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya, da jami'an zaunannen kwamitin ofishin siyasa da babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar. An kuma zartas da mambobin ofishin sakataren kwamitin tsakiyar JKS da amince da kusoshin kwamitin soja da kwamitin ladabtarwa da da'a. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China