in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#JKS19# Xi Jinping: dole ne 'yan JKS su kasance ginshikan jagororin bauta wa al'ummar kasa
2017-10-25 13:22:42 cri

Yau Laraba ne Xi Jinping, babban sakataren JKS ya bayyanawa manema labaru na gida da wajen cewa, shekarar 2021, shekara ce ta cika shekaru 100 da kafuwar JKS. JKS ta dade tana himmantuwa kan muhimman al'amuran da suka shafi al'ummar Sinawa. Ya ce, jam'iyyar na cikin kuruciyarta yayin ta cika shekaru 100 da kafuwarta. A don haka ya zama tilas 'yayan JKS su kasance masu kuruciya, jagorori, masu kishin kasa, kana bauta wa jama'a har abada. Xi ya kuma jaddada cewa, za a dauki tsattsauran matakai kan tafiyar da harkokin jam'iyyar daga dukkan fannoni, aikin da ba shi da karshe. Dole ne a tsaya kan nuna adalci a yanayin tafiyar da harkokin siyasa, a kokarin ganin kyakkyawan hadin gwiwar 'yan jam'iyyar sun karfafa gwiwar daukacin al'ummar kasa yayin da ake kokarin bunkasa kasar ta Sin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China