in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabunta: An rufe taron JKS karo na 19
2017-10-24 13:45:15 cri
A ranar Talatar nan ne Babban sakataren JKS Xi Jinping ya sanar da samun nasarar rufe babban taron wakilan JKS karo na 19.

An kammala taron ne, bayan da aka kammala zaben sabbin mambobin kwamitin koli da na kwamitin ladabtarwar jam'iyyar.

A daya hannun kuma wakilai mahalarta taron, sun zartas da kuduri game da rahoton da kwamitin koli na taron jam'iyyar karo na 18 ya gabatar. Kaza lika an amince da gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin jam'iyyar, wanda aka sanya "Tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki" a matsayin jigon zartas da muradun JKS bisa salo na musamman na gurguzu mafi dacewa da yanayin kasar Sin. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China