in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#JKS19# Xi Jinping: yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje na da matukar muhimmanci ga kasar Sin
2017-10-25 13:00:07 cri

Yau Laraba ne Xi Jinping, babban sakataren JKS ya bayyanawa manema labaru na gida da wajen cewa, shekara mai zuwa, shekaru 40 ke nan da kasar Sin ta fara aiwatar da yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, matakin da yake da muhimmanci matuka ga kasar Sin a wannan zamani. JKS za ta takaita fasahohinta, za kuma ta ci gaba da zamanintar da tsarin tafiyar da harkokin kasa da inganta karfinta na tafiyar da harkokin kasa, tare da nacewa kan zurfafa yin gayre-gyare a gida da bude kofa ga waje, a kokarin ganin matakan yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje suna taimakawa da kuma karfafa gwiwa ga juna. Xi ya yi imani da cewa, tabbas za a inganta rayuwar al'ummar Sin yayin da ake aiwatar da shirin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China