Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin ya shiga wani sabon zamani, biyo bayan kokarin da aka dade ana yi, don haka ya kamata a bullo da sabbin abubuwa a wannan zamani, don samun sabbin nasarori. A shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta tabbatar da ganin kafa zaman al'umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni a yayin da JKS ta cika shekaru 100 da kafu, tare da fatan ganin za a soma cimma burin kafa kasar Sin mai tsarin gurguzu ta zamani mai wadata, bin tsarin demokuradiya, wayin kai da kuma jituwa nan da shekara 2049, wato yayin bikin cika shekaru 100 da kafa jamhuriyar Jama'ar Sin. (Bilkisu Xin)