171023-kasar-sin-za-ta-kara-samar-da-gudunmowa-ga-cigaban-duniya-bello.m4a
|
A watan Agusta, kamfanin ba da shawara kan harkoki masu alaka da kasuwa na Ipsos na kasar Faransa, ya gudanar da wani binciken ra'ayin jama'a a kasashe 26 da suka hada da Sin, da Amurka, da Birtaniya, da Japan da dai sauransu, don jin ra'ayin al'umma kan ci gaban kasarsu. Inda sakamakon da aka samu ya nuna cewa, kashi 87% na al'ummar kasar Sin na sa ran ganin ci gaban kasarsu cikin sauri a nan gaba, jamillar da ta kasance mafi girma, idan an kwatanta da sauran kasashen da aka gudanar da binciken. Hakan, a cewar wasu kafofin watsa labaru na kasashe daban daban, na taimakawa daidaita yanayin da ake ciki na fama da rashin tabbas kan yanayin tattalin arzikin duniya.
A ganin Sergey Luzianin, shugaban sashen nazarin yankin gabashin duniya karkashin cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Rasha, kasar Sin ta samu nasarori a fannonin da suka hada da kirkiro sabbin dabarun raya tattalin arziki, da hadin gwiwa tare da sauran kasashe. Hakan ya samu ne saboda tsarin gurguzu na musamman da kasar ke bi. Haka zalika, ya ce shirye-shiryen da aka gabatar wajen taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19 sun zama wani misali ga sauran kasashe. A cewarsa,
"Tsarin musamman da kasar Sin ta dauka ba ma kawai ya taimakawa ci gaban tattalin arzikin kasar ba ne, har ma ya zama abin koyi ga sauran kasashe, inda jama'arsu ke kokarin zamanintar da tattalin arziki."
Ban da haka, kasar Sin ta zame ma duniya abin koyi a fannin yaki da cin hanci da rashawa. Simon Khaya Moyo, ministan watsa labarai na kasar Zimbabwe, ya ce ayyukan da kasar Sin ta gudanar a wannan fanni na da burgewa.
"Na girmama jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin kan matakan yaki da cin hanci da rashawa da ta dauka. A kasar Zimbabwe, gwamnati ita ma tana kokarin shawo kan matsalar cin hanci da rashawa, sai dai aikin yana da wuya. Ya kamata mu koyi daga fasahohin da kasar Sin ta samu a wannan fanni."
Cikin rahoton da aka gabatar wajen taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19, an nanata cewa, an kafa jam'iyyar ne don tabbatar da moriyar jama'ar kasar Sin, da kuma neman taimakawa ci gaban al'amuran duniya da suka shafi daukacin dan Adam. Bisa wannan zancen, Madam Vandee Boutthasavong, jakadar kasar Laos a kasar Sin, ta nuna amincewa.
"Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin tana son zaman lafiya, da kokarin neman ci gaban kasa, da hadin gwiwa, da yunkurin amfanawa juna. Manufar diplomasiyyar da kasar Sin ke dauka ta neman sulhu, da dogaro da kai tana samar da gudunmowa ga kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya."
Haka zalika, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta jaddada a cikin rahotonta ra'ayin kula da harkokin duniya na tattauna tsakanin bangarori daban daban, da raya duniya, da more sakamakon da aka samu tare. A ganin Laurie Pearcey, mataimakin shugaban jami'ar New South Wales ta kasar Australia, kasar Sin za ta iya taimakawa kokarin dunkule bangarorin duniya a waje guda.
"Mun lura da cewa, Xi Jinping ya ambaci shirin kasar Sin na kara taka rawa wajen kula da harkokin duniya. Yanzu haka idan shugabannin kasar Sin sun yi magana kan tattalin arzikin kasar, da yanayin siyasar kasar, duniya za ta saurara. Kasar Sin tana kara zama mai fada a ji a duniya, da kara taka wata muhimmiyar rawa a fannin kula da harkokin kasa da kasa."
A nata bangare, Madam Lydia Samarbakhsh, jami'a mai kula da hulda da jam'iyyun kasashe daban daban ta jam'iyyar Kwaminis ta kasar Faransa, ta ce rahoton jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya nuna niyyarta ta sauke nauyin dake bisa wuyanta a fannin daidaita al'amuran duniya. Ta ce,
"Yanzu ana kara samun bambancin ra'ayi tsakanin kasashe daban daban, sai dai shawarwarin da kasar Sin ta gabatar kan kula da duniya da neman ci gaba cikin lumana, za su iya taimakawa hada kawunan kasashen. Ba wanda zai iya rayuwa tare da mutunci shi kadai, tilas ne ya yi hadin gwiwa da saura. Hakan na bukatar kowanenmu ya yi kokarin kawar da sabanin ra'ayi a fannin siyasa, da daidaita yanayin da ake ciki."(Bello Wang)