171018-xi-jinping-ya-gabatar-da-rahoto-a-taron-jks-karo-na-19.m4a
|
Yau Laraba 18 ga wata, aka kaddamar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 a nan birnin Beijing. A madadin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na 18, babban sakatare Xi Jinping, ya gabatar da wani muhummin rahoto a yayin bikin kaddamar da taron, inda ya sanar da cewa, gurguzu mai tsarin musamman na kasar Sin ya shiga wani sabon mataki, lamarin da yana da ma'anar tarihi ga ci gaban kasar ta Sin.
Yanzu yanayin duniya yana samun manyan sauye-sauye, a saboda haka sabbin manufofin da jam'iyya mai mulki a kasar Sin wadda take samun saurin bunkasuwar tattalin arziki za ta aiwatar a nan gaba sun jawo hankulan al'ummun kasashen duniya, inda babban sakatare Xi Jinping ya bayyana cewa, "Babban taken taro na yau shine kada mu manta hakkin dake rataye a wuyanmu, bari mu sanya kokari tare domin tabbatar da gurguzu mai tsarin musamman na kasar Sin da al'umma mai wadata a sabon zamanin da muke ciki, ta yadda za mu cimma burinmu na farfado da al'ummar kasar Sin cikin nasara."
A cikin rahoton da Xi ya gabatar, ya bayyana cewa, a cikin shekaru biyar da suka gabata, jam'iyyar kwaminis ta kasar tana kara karfafa karfin jagoranci a fadin kasar, har ta fitar da wasu sabbin manufofin tafiyar da harkokin kasa, don haka an samu babban sakamako daga dukkan fannoni a kasar ta Sin, misali adadin karuwar GDP ya kai yuan biliyan dubu 80, adadin da ya kai kaso 30 bisa dari daga cikin kwatankwacin karuwar tattalin arzikin duniya, kana a kowace shekara adadin karuwar guraben aikin yi a garuruwa da biranen kasar ya kai sama da miliyan 13, ban da haka kuma adadin al'ummun kasar wadanda suka kubuta daga kangin talauci ya zarta miliyan 60. Abu mai faranta ran mutane shi ne tun bayan da aka kara zurfafa kwaskwarima daga dukkan fannoni a kasar Sin, sai ta samu babban ci gaba wajen tabbatar da demokuradiya da wayewar kai, da gudanar da harkokin kasa bisa doka, da 'yantar da tunanin al'ummun kasa, da kyautata zaman rayuwar al'uumun kasar da sauransu, inda babban sakatare Xi Jinping ya bayyana cewa, "Bayan kokarin da aka yi cikin dogon lokaci, gurguzu mai tsarin musamman na kasar Sin ya shiga sabon zamani, ana iya cewa, muna cikin wani zamani mai muhimmanci matuka, saboda muna kokarin tabbatar da al'umma mai wadata tare kuma da gina wata babbar kasar gurguzu mai tsarin musamman, ta yadda kuma kasar Sin za ta kara taka rawa a cikin harkokin duniya kamar yadda ake fata."
Xi ya ci gaba da cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da al'ummar kasar zasu ci gaba da nacewa da kuma raya tunanin gurguzu mai tsarin musamman na kasar Sin a sabon zamanin da muke ciki, inda ya kara da cewa, "Nacewa kan tunanin gurguzu mai tsarin musamman na kasar Sin shi ne domin zamanintar da gurguzu da farfado da al'ummun Sinawa bisa tushen tabbatar da al'umma mai wadata a fadin kasar, to idan ana son cimma burin, dole ne a kara maida hankali kan banbance-banbancen dake tsakanin bukatar jin dadin rayuwar al'ummar kasar da irin rashin daidaito ta fuskar ci gaba da ake fuskanta a kasar, kana dole ne a ba da muhimmanci kan babbar moriyar al'ummun kasa, ta haka za a tabbatar da wadata tare daga dukkan fannnoni a fadin kasar ta Sin."
Kazalika, babban sakatare Xi ya jaddada cewa, duk da cewa an samu ci gaba yayin da ake kokarin yaki da cin hanci da rashawa, amma ya zama wajibi a kara nuna kwazo da himma kan aikin gudanar da harkokin jam'iyyar, ya ce, "Al'ummun kasa sun fi kyamar cin hanci da rashawa, matsalar tana kawo babbar illa ga jam'iyyarmu, shi ya sa dole ne mu cigaba da sanya kokari matuka domin dakile matsalar yadda ya kamata, ta haka kuma za a cimma burin tabbatar da kwanciyar hankali a kasar cikin dogon lokaci"(Jamila)