in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin kasar Sin na kara yin hadin gwiwa da kasashen duniya
2017-10-23 13:31:06 cri

Gyare-gyaren da aka yi a 'yan shekarun baya a cikin rundunar sojin kasar Sin ya janyo hankulan duniya sosai. Ba ma kawai an dauki matakan yin gyare-gyaren da ba a taba ganinsu a da ba, har ma yanzu a kan ga sojojin kasar Sin wadanda suke shiga ayyukan tabbatar da zaman lafiya a kasashe daban daban. A yayin wani taron manema labaru da aka shirya a jiya Lahadi, wakilai hudu daga rundunar sojin kasar Sin dake halartar babban taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 da ake yi a nan Beijing suna ganin cewa, sabon yanayin yin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya yana samun karbuwa a kai a kai. A matsayinsu na sojin kasar Sin, sun bayyana cewa, za su ci gaba da yin kokarin iya karfinsu domin samar da tsaro a duk duniya.

"Na gamsu da matakan kasar Sin, na kuma gode wa sojojin ruwan kasar Sin. Idan jaririna ya girma, tabbas e zan gaya masa cewa Sinawa ne suka ceto shi suka kuma kawo shi duniyar nan."

Wannan kalaman wata mahaifiya ce a kasar Saliyo da ake kira Lamando. A watan Satumban bana, jaririn da Lamando take dauke da shi ya samu hadari, amma ya yi sa'a, an kai Lamando jirgin sojojin ruwan kasar Sin mai aikin ba da jinya kyauta na "Peace Ark" wanda yake aikin ba da hidimar aikin jinya a kasar Saliyo. Likitocin rundunar sojin kasar Sin sun taimakawa Lamando ta haifi jaririnta lami lafiya. Sabo da haka, Lamando da mijinta suka rada masa suna "Zaman lafiya".

Wannan karamin labari na rundunar sojin kasar Sin ya girgiza kasashen duniya. A cikin shekaru 5 da suka gabata, yawan abokan rundunar sojin kasar Sin yana ta samun karuwa, tana kuma kokarin samar da karin kayayyakin tsaro ga sauran kasashen duniya. Madam Liu Fang, wata hafsa ce dake aiki a ofishin yin mu'amala da hadin gwiwar harkokin soja da sauran kasashen duniya na kwamitin tsakiyar rundunar sojin kasar Sin, tana ganin cewa, tuni aka kafa wani sabon yanayin yin hadin gwiwar kasa da kasa a fannin soja daga dukkan fannoni. Madam Liu Fang tana mai cewa, "Muna kokarin sauke nauyin da aka dora wa wata babbar kasa kamar yadda ya kamata. A kullum muna nuna goyon baya ga harkokin wanzar da zaman lafiya na MDD. Sannan muna kuma kokarin taimakawa sauran kasashen duniya wajen tinkarar bala'u daga indallahi. Bugu da kari, muna gudanar da aikin tsaron jiragen ruwa a ketare. Ya zuwa yanzu, yawan jiragen ruwan kasar Sin da na sauran kasashen duniya da muka samar wa tsaro ya kai fiye da 6300."

A hakika, dalilin da ya sa rundunar sojin kasar Sin ta iya sauke nauyin da ke bisa wuyanta shi ne, ta samu ci gaba da karfi a cikin shekaru 5 da suka gabata. A cikin wadannan shekaru 5 da suka gabata, an dauki kwararan matakai da dama wajen yiwa rundunar sojin kasar Sin da aikin tsaron kasar gyaran fuska. Rundunar sojin kasar Sin ta fi mai da hankali kan yadda za a kara karfinta na shiga yaki domin tsaron iyakokin tekun kasar, da yaki da ta'addanci da samar da zaman lafiya, da tinkarar bala'u daga indallahi, da tabbatar da zaman lafiya a ketare, da tsaron jiragen ruwan fararen hula a yankin tekun Aden, da kuma samar da taimakon jin kai a ketare. Bugu da kari, makamai da na'urorin soja ma sun samu kyautatuwa.

Mr. Liu Rui, jami'in mai kula da wata karamar bataliya, kuma wani tsohon matukin jirgin saman yaki ya kan halarci ayyukan samun horo da a kan yi a can saman tekun Pacifik, yana mai cewa, "A da, na halarci ayyukan horaswa wajen sau 4 a cikin shekara daya. Amma yanzu a kan shirya ayyukan samun horo da dama a wata guda. Sannan, a da, na kan tuka jirgin saman yaki iri daya ne kawai, amma yanzu a lokacin da muke yin ayyukan samun horo mu kan tuka jiragen saman yaki iri daban daban, kamar jirgin saman yaki da jirgin saman dake karawa jirage mai a sama da jirgin saman farautar bayanan asiri da kuma jirgin saman aikewa da gargadi. Bugu da kari, yanzu mu kan yi aikin horaswa a can saman yankin tekun Pasifik kamar yadda za mu shiga wani hakikanin yaki. Dalilin da ya sa muka yi haka shi ne kara karfinmu na aikin soja ta yadda za mu gudanar da ayyukanmu kamar yadda ya kamata."

A cikin rahoton siyasa na babban taron JKS karo na 19, an jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da martaba manufar tsaron kasa, ko da yake kasar Sin na samun ci gaba, amma ba za ta kawo barazana ga sauran kasashen duniya ba. Gamayyar kasashen duniya na ganin cewa, ci gaban da rundunar sojin kasar Sin ta samu, ci gaban rundunar tabbatar da zaman lafiyar kasa da kasa ne. Amma, a waje daya, wadannan wakilan rundunar sojin kasar Sin sun bayyana cewa, tabbas rundunar sojin kasar Sin za ta yi amfani da karfinta a matakai daban daban wajen tsaron 'yancin kasa da kwanciyar hankali da kuma 'yancin neman samun ci gaba na kasar Sin cikin lumana. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China