in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban jam'iyya a Morocco: JKS ta zama abun koyi ga kasashe masu tasowa
2017-10-23 09:38:47 cri

Shugaban jam'iyya ta biyu mafi girma a Morocco Habib Belkouch, ya ce Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta zama misali ga kasashe maso tasowa wajen jagorantar al'ummarsu bisa tafarkin da ya dace.

Habib Bellkouch ya ce, jam'iyyarsa ta Authenticity and Modernity, na bibiyar babban taron JKS karo na 19, da aka bude ranar Laraba da ta gabata da zai shafe mako guda ana yi a nan birnin Beijing, wanda ya kasance wani muhimmin taron siyasa na kasar Sin cikin shekaru 5.

Da yake tsokaci game da ci gaban da kasar Sin ta samu cikin gomman shekarun da suka gabata, Belkouch ya tuna da ziyararsa a kasar dake nahiyar Asiya, inda ya ce, ya yi mamaki matuka.

Ya ce, ganin yadda ake jagorantar jama'a kimanin biliyan 1.4, da yadda kasar ta samu damar cimma dukkan wadannan ci gaba a cikin shekaru 30, babu abun da ya kamata a yi face yabawa rawar da JKS ta taka, da kuma shugaban kasar da ya jagoranci samar da nasarorin.

Da yake bayyana kudurin jam'iyyarsa ta kafa tarihi a kasar a bayyane kuma bisa zamani, ya ce yadda kasar Sin ta hade zamani da gargajiya wajen zamanantar da kasar, ya burge shi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China