in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNAMID ta rage yawan dakaru a Darfur na Sudan
2017-10-23 09:49:10 cri

Tawagar kiyaye zaman lafiya ta MDD a yankin Darfur (UNAMID) ta sanar da rage yawan dakarunta dake aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur na kasar Sudan.

Kimanin dakarun soji 1,440 da kuma 'yan sanda 240 ne aka janye su daga bakin daga, bisa mutunta sabon kudurin da kwamitin tsaron MDD mai lamba 2363 ya amince da shi.

Mai magana da yawun UNAMID Ashraf Eissa, ya bayyana a taron manema labarai cewa, tun farkon sauya fasalin wannan shiri ne, manyan bataliyoyin sojin kiyaye zaman lafiya na kasashen Najeriya da Pakistan, kowannensu na da adadin dakaru 720, aka rage yawan dakarun.

Kakakin ya bayyana cewa, a cikin wannan lokaci, tawagar UNAMID zai rufe wasu sansanonin dakarun kiyaye zaman lafiyar 11 a duk fadin yankin na Darfur bisa sabon matakin kwamitin tsaron MDD mai helkwatar a birnin New York.

A halin yanzu, kwamitin tsaron MDD ya amince da sabon kuduri mai lambar 2363, inda ya mayar da tsarin aikin UNAMID zuwa zango biyu, kowane zango za'a shafe tsawon watannin 6 ne.

An yi amanna cewa, UNAMID ita ce tawagar kiyaye zaman lafiya ta MDD mafi girma a duniya, baya ga wadda ke jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC.

A shekarar 2008 ne aka tura tawagar UNAMID zuwa yankin Darfur, yankin dake fama da tashe tsahen hankula tsakanin dakarun sojin kasar Sudan da 'yan tawaye sakamakon wani kazamin fada da ya barke tun a shekarar 2003.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China