in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD da AU sun yi Allah wadai da hari kan jami'an UNAMID a Darfur
2016-03-11 10:16:28 cri

MDD da kungiyar tarayyar Afrika AU sun yi Allah wadai da kaddamar da hari na baya bayan nan kan jami'an aikin wanzar da zaman lafiya na UNAMID a yankin Darfur na kasar Sudan, lamarin da ya haddasa mutuwar wasu daga cikin jami'an, tare da jikkata wasu.

Shugabar kwamitin tarayyar Afrikan Nkosazana Dlamini-Zuma, da sakatare janar na MDD Ban Ki-moon, sun yi Allah wadai da kaddamar da wannan harin wanda wasu dake dauke da makamai da ba'a tantance su ba suka aiwatar.

Harin dai ya faru ne a wurin da ke da tazarar kilomita 40 daga kudu maso yammacin Kutum dake arewacin Darfur, a lokacin da jami'an ke gudanar da aikin sunturi tsakanin Kutum zuwa Djarido.

Ban Ki-moon da Zuma, sun bukaci bangarorin da ba sa ga maciji da juna a yankin Darfur da su mutunta tawagar jami'an aikin wanzar da zaman lafiyar.

Bugu da kari sun bukaci gwamnatin Sudan da ta gudanar da bincike domin zakulo wadanda ke hannu wajen kaddamar da harin domin hukunta su.

Sannan sun gabatar da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, tare da yin fatar samun sauki daga wadanda suka jikkata a harin.

Tun a shekarar 2008 ne jami'an aikin wanzar da zaman lafiyar ke fuskatar hare hare, kuma kawo yanzu adadin jami'an da aka hallaka ya kai 61.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China