in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta girke karin dakaru a yankin Darfur
2015-07-07 09:46:40 cri

Mahukuntan kasar Sudan sun kara yawan dakarun soji a yankin gabashin Darfur mai fama da yawan tashe-tashen hankula tsakanin kabilu.

Hakan, a cewar gwamnan jihar gabashin Darfur Anas Omer, ya biyo bayan karuwar fadace-fadace ne tsakanin kabilun dake jihar. Ya ce, gwamnatin kasar ta jibge karin sojoji kusan 1,800 domin tabbatar da kyakkyawan yanayin tsaro da dakile barkewar rikici. Omer ya kara da cewa, baya ga dakile tashe-tashen hankula, dakarun sojin kasar wadanda ke dauke da cikakkun kayan aiki, za kuma su sanya ido kan sauran fannonin tsaro da suka hada da kare harkokin noma, da burtalolin makiyaya, da kuma tsaron hanyoyin dake hada yankin da birnin Khartoum, fadar mulkin kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China