in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta haramtawa hukumomin kasa da kasa shiga yankin Darfur
2016-02-22 10:01:54 cri

Mahukuntan kasar Sudan sun haramtawa hukumomin MDD da na kasa da kasa shiga yankin Darfur, saboda abin da suka kira dalilai na tsaro.

Karamin minista a ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sudan Kamal-Eddin Ismail wanda ya shaida haka ga taron manema labarai a jiya Lahadi, ya ce, matakin hana wadannan hukumomi shiga yankin na wucin gadi ne. Sai dai ya ce, ba hana hukumomin zirga zirga a yankin ba.

Minista Kamal ya nanata cewa, wajibi ne hukumomin su rika martaba dokokin gwamnatin Sudan kamar yadda suka cimma yarjejeniya da gwamnatin.

Tun da farko ofishin kula da harkokin jin kai na MDD da ke Sudan ko OCHA a takaice ya bayyana cikin wani rahoto cewa, hukumomin bayar da agaji na gida da na ketare ba sa iya tantance sabbin mutanen da suka rasa matsugunansu da yanzu haka suka iso tsakiyar yankin Darfur daga Jebel Marra.

MDD da sauran hukumomin kasa da kasa sun sha kokawa kan yadda mahukuntan Sudan ke hana su kaiwa ga dubban mutanen da suka rasa matsugunansu sakamakon fadan da sojojin suke gwabzawa a Jabel Marra da ke yankin Darfur.

Tun a tsakiyar watan Janairun shekarar da ta gabata ce fada ya barke a yankin Jebel Marra da ke tsakiyar jihar Darfur na Sudan tsakanin sojojin Sudan da dakarun 'yan tawayen SLM reshen Abdul-Wahid Nur.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China