in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Sudan sun dakile wani hari daga 'yan adawa a Darfur
2015-04-27 15:12:19 cri

A ranar Lahadin nan, gwamnatin kasar Sudan ta sanar da cewar, sojojinta sun yi nasarar dakile wani hari a kan jihar kudancin Darfur wanda 'yan adawar da kasar Sudan ta Kudu ke marawa baya suka yi niyyar kai wa.

Kakakin sojin kasar Al-Sawarmy Khalid Sa'ad ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar wa manema labarai, ya ce, sojojin Sudan din sun kwace motoci 100 lokacin da su kuma 'yan adawar suka tsere tare da barin 'yan uwansu da dama da aka kashe.

A wani bangaren kuma sojojin sun zargi kasar Sudan ta Kudu da boye tare da horas da kungiyoyin adawa, suna musu cewa, kungiyar JEM tana ta horas da 'yan kasashen waje fiye da watanni ke nan a yankin Raja dake jihar Bahral Ghazal a kasarta.

Ya yi bayanin cewa, 'yan adawar sun yi shirin kai hari a rijiyoyin mai, bankuna, kasuwanni a wurare daban daban. A ranar Asabar ne dai gwamnan kudancin Darfur Adam Mahmoud Jaral-Nabi ya bayyana cewa, jami'an tsaro na matakan gaggawa karkashin hukumar leken asiri ta kasar sun tabbatar da cewar, sun gano dakaru masu yawa mallakar kungiyar ta JEM da kuma SLA suna shiga kudancin Darfur daga Sudan ta Kudu.

Sudan dai tana zargin Sudan ta Kudu da taimakawa tare da ajiya rundunar RFA wadanda suke tare da manyan kungiyoyin 'yan tawaye guda 3 a Darfur, ban da SPLM na arewacin kasar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China