171021-Xia.mp4
|
'Ta hanyar watsa ingantattun labarai ne, jama'a daga kasashe daban-daban za su iya kara fahimtar halayyar mutanen sauran kasashe da na kabilu, da sanin hanyoyin da suke bi wajen neman ci gaba da yadda tsarin zamantakewar al'ummarsu yake', in ji Xia Yongmin, wani wakilin babban taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, kana shugaban cibiyar watsa labarai zuwa yankunan yammacin Asiya da Afirka ta CRI. Ga abun da ya fada:
Barka, abokanmu manema labarai, sunana Xia Yongmin, na yi karatun harshen Turkiyya a jami'a, kuma yanzu aikina shi ne, watsa labarai zuwa kasashe da yankuna daban-daban.
Idan za ku iya tunawa, a shekarar 2013, yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke ziyarar aiki a kasar Tanzaniya, ya yi bayanin cewa, wani shirin talabijin na kasar Sin mai suna Doudou da surukanta, wanda aka fassara daga harshen Sinanci zuwa harshen Swahili, ya samu karbuwa sosai bayan da aka nuna shi ta gidan talabijin na Tanzaniya, ta dalilin wannan shiri, jama'ar kasar sun samu damar kara fahimtar yadda zaman rayuwar Sinawa yake.
Shi ya sa nake ganin cewa, al'adu na samar da muhimmiyar hanya da dandali da jama'a za su karfafa dankon zumunci da fahimtar juna tsakaninsu, kuma wani muhimmin sashi ne na harkokin watsa labarai zuwa kasashen waje.