A nasa bangaren, wani wakilin jam'iyyar, kana, shugaban cibiyar watsa labarai zuwa yankunan yammacin Asiya da Afirka ta gidan rediyon kasar Sin CRI, Mista Xia Yongmin ya ce, al'adu na samar da muhimmiyar hanya da dandali da jama'a za su karfafa dankon zumunci da fahimtar juna tsakaninsu, kuma wani muhimmin sashi ne na harkokin watsa labarai zuwa kasashen waje. Mista Xia ya ce, a 'yan shekarun nan, gidan rediyon CRI ya shirya wasu ayyukan mu'amala ta fuskar al'adu da dama, ciki har da fassarar fina-finan kasar Sin zuwa harsuna daban-daban, abun da ya taimaka sosai ga cudanyar al'adu tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya.
A 'yan shekarun nan, sakamakon ingantuwar tattalin arziki da kyautatuwar zaman rayuwar al'umma a kasar Sin, ana kara samun kasashe da yankuna daban-daban, wadanda ke bayyana niyyarsu ta fahimtar kasar Sin. Rahoton da aka fitar yayin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis a wannan karo, ya ce kamata ya yi a habaka cudanya da mu'amala ta fuskar al'adu, domin nunawa duniya yadda kasar Sin take daga dukkanin fannoni.
Dangane da haka ne, Mista Xia Yongmin ya ce, ya kamata a yi kokarin gano nagartattun al'adu na kasashe daban-daban. Ya na mai cewa ta hanyar watsa labarai kan wadannan al'adu ne, jama'a za su kara fahimtar halayyar kabilar Sinawa ko kasar Sin tare da kara sanin hanyar da kasar ke bi wajen neman ci gaba da tsarin zamantakewar al'ummarta. (Murtala Zhang)