in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilan kungiyar 'yan jarida ta Afirka: ya kamata a koyi muhimman fasahohin kasar Sin
2017-10-19 14:43:58 cri
A jiya Laraba ne, wasu wakilan 'yan jarida daga kasashen waje suka saurari rahoton da babban sakatare Xi Jinping ya gabatar a madadin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a gun babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 da aka bude a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing. Tun a ranar 16 ga wannan wata ne, wakilan suka kalli jiragen kasa mafi saurin tafiya, da kekunan haya, da kai ziyara yankin Binhai na birnin Tianjin da unguwar kirkire-kirkire ta Zhongguancun dake birnin Beijing. Wakilai 5 na kungiyar 'yan jarida ta Afirka wadanda suka zo daga Sudan, Kenya, Nijeriya, Tanzania da kuma Afirka ta Kudu sun kara sanin bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin, a ganinsu, ya kamata kasashen Afirka su koyi muhimman fasahohin da kasar Sin ta yi amfani da su wajen samun wadannan ci gaba. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China