Shugaban kasar Nijer Mahamadou Issoufou ya bayyana a cikin wasikarsa cewa, wannan taro zai tsaida makomar kasar Sin da ta dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen duniya, da sa kaimi ga kasar Sin da ta samu ci gaba da wadata. Ana da kyakkyawar makomar hadin gwiwa dake tsakanin Nijer da Sin, kasar Nijer ta rike damar hadin gwiwa don sa kaimi ga aiwatar da shirin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma.
A nasa bangaren, shugaban kasar Sudan kuma shugaban jami'iyyar NCP Omar al-Bashir, ya bayyana a cikin wasikarsa cewa, ya yi imani da raya dangantakar dake tsakanin kasarsa ta Sudan da kasar Sin, da shiga sabon lokacin samun ci gaba. Kana ya taya murnar gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 cikin nasara.
Shugabannin kasashen Tanzania da Burundi, Namibia, Afirka ta Kudu, Ruwanda da sauransu su ma sun buga waya ko mika wasiku don taya murnar gudanar da taron. (Zainab)