Jiya Laraba, aka bude babban taron wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin CPC karo na 19 a nan birnin Beijing, inda babban sakataren jam'iyyar Xi Jinping, ya gabatar da rahoto. Inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu manyan nasarori a fannonin bude kofa ga waje da yin kwakwarima a gida da kuma inganta rayuwar al'umma karkashin tsarin gurguzu a cikin wadannan shekaru biyar da suka gabata, hakan ya sa aka bude wani sabon shafi ga ci gaban jam'iyyar CPC da sha'anin raya kasar.
Game da batun, 'yan siyasa da masana daga kasashe daban daban sun jinjinawa manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a karkashin jagorancin jam'iyyar CPC da kuma dabarun da kasar Sin ta samar don warware matsalolin da duniya ke fuskanta.
Game da nasarar da kasar Sin ta samu a fannonin fama da kangin talauci da ci gaban birane, tsohon firaminitan kasar Masar Essam Sharaf, yana ganin cewa, wannan shi ne muhimmin kashi na burin kasar Sin. A cewarsa, nasarar ta sheda daidaiton bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, wadda ta amfana wa kowa da kowa.
Farfesa Khairy Tourk, na jami'ar fasaha ta Illinois da ke kasar Amurka ya kuma nuna cewa, kasar Sin tana ta samun karuwar tattalin arziki, kuma tana da aniyar more muradun tattalin arzikin da ta samu tare da sauran kasashe ta hanyar gabatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya". Shawarar kuwa ta kasance daya daga cikin manyan ayyukan a tarihin duniya, wadda za ta ba da muhimmin tasiri ga tattalin arzikin duniya.
A nasa bangaren, Garrishon Ikiara, malamin koyar da ilmin tattalin arziki na jami'ar Nairobi ta kasar Kenya yana ganin cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba wajen tattalin arziki da zamantakewar al'ummarta, kuma tana ta taka muhimmiyar rawa a duniya. Duk wadannan nasarori na da alaka da manufofin Jam'iyyar CPC masu basira da shugabancin jam'iyyar yadda ya kamata. Hakan ya sheda nagartar hanyar gurguzu mai halin musamman da kasar Sin ke bi.(Kande Gao)