Rahoton Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya nuna cewa, kasar Sin za ta kara kafa hukumomin sa ido a fannonin gudanar da harkokin mulkin kasa bisa doka da kiyaye muhalli da aikin soja da dai sauransu. Wadanda suka hada da kafa kungiyar shugabanni ta aikin gudanar da harkokin mulkin kasa bisa doka, da hukumar sanya ido kan aikin gudanar da albarkatun kasa da muhallin halittu, da hukumar sanya ido a matakai hudu wato na kasa da lardi, da birni, da kuma na gunduma, domin sa ido kan dukkan ma'aikatan gwamnati da yaki da cin hanci da rashawa. Bugu da kari za a kafa hukumar kula da sojojin da suka yi ritaya don tabbatar da kiyaye muradunsu bisa doka. (Kande Gao)