in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#JKS19#Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin za ta nace ga kokarin dakile cin hanci da rashawa
2017-10-18 13:18:15 cri
Babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping, ya furta a wajen taron wakilan jam'iyyar karo na 19 cewa, jama'ar kasar Sin suna kin jinin cin hanci da rashawa matuka, kana batun cin hanci da rashawa shi ne barazana mafi tsanani da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin take fuskanta. Saboda haka, jam'iyyar za ta nace ga manufarta na sa ido kan dukkan 'ya'yanta da jami'ai manyan da kanana, inda ba za ta yi sassauci ga duk wanda ya aikata laifin ba. Sa'an nan za a tsaya kan binciken wadanda suka aikata cin hanci da wadanda suka karba a lokaci guda, da magance samun kungiyoyi masu neman riba ta haramtacciyar hanya tsakanin 'ya'yan jam'iyyar. Za a kafa tsarin rangadi da sa ido a kwamitocin jam'iyyar a matsayin birane da gundumomi, da karfafa kokarin dakile cin hanci da rashawa da ya yi mummunar tasiri ga zaman rayuwar jama'a.

Xi Jinping ya ce, duk inda masu aikata zamba suka gudu, za a bi su kuma a kama su don gurfanar da su gaban kotu. Sa'an nan za'a kara kafa wasu dokokin da suka shafi aikin yaki da cin hanci da rashawa, da kuma kafa dandalin kai kara a hukumomin sa ido da ladabtarwa na matakai daban daban.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China