in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#JKS19#Kasar Sin za ta kara kokarin kyautata muhallinta
2017-10-18 13:15:19 cri
Babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping, ya furta a wajen taron wakilan jam'iyyar karo na 19 da ke gudana a birnin Beijing na kasar cewa, kasar za ta kara kokarin kafa wasu manufofi da ka'idoji masu alaka da samar da kayayyaki tare da yin amfani da su ba tare da gurbata muhalli ba, da kokarin gina wani tsarin tattalin arziki da ya maida hankali kan rage iska mai gurbata muhalli da ake fitarwa, da tattalin arzikin bola-jari, da tsarin hada-hadar kudi irin na kare muhalli.

Xi Jinping ya kara da cewa, kasar Sin za ta kara kokarin tsabtace iska, da ruwa, da kuma filayen noma, da rage fitar da sinadarai masu gurbata muhalli, da kokarin halartar ayyukan da ke gudana a duniya na daidaita muhalli, don daidaita wasu manyan matsalolin da yanzu haka ake fuskantar a wannan fanni.

Haka zalika za a gudanar da wasu manyan ayyukan da suka shafi karewa da daidaita muhalli, da kafa tsarin biyan diyya a yayin da aka samu tasirin gurbata muhalli. Ban da haka kuma, za a kafa hukumomi masu sa ido kan albarkatun kasa mallakar gwamnati da yanayin muhalli da halittu, da kafa tsarin kare filayen da kasar ke da su, da tsarin kare muhalli na kebe yankunan kare halittu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China