#JKS19# Mazaunan kauyuka masu fama da talauci za su fita daga kangin talauci a shekarar 2020
A cikin rahoton da babban sakatare Xi Jinping ya gabatar a gun babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 19, an jaddada cewa, za a tabbatar da kawar da talauci a dukkan yankunan karkara gaba daya a shekarar 2020 bisa ma'aunin Sin da ake aiwatarwa a halin yanzu, da warware matsalar fuskantar talauci a yanki, da tabbatar da kawar da talauci yadda ya kamata. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku