#JKS19#Kasar Sin ta bayyana tsarinta na tabbatar da lafiyar jikin jama'a daga dukkan fannoni a karon farko
Cikin rahoton da babban sakataren jami'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a wajen taron wakilan jam'iyyar karon 19 dake gudana a birnin Beijing na kasar, an ce za a kafa wani tsari mai inganci na aikin jinya da tabbatar da lafiyar jikin jama'a iri na musamman na kasar Sin. Karkashin wannan buri ne za a kara horar da likitocin dake aiki a cikin kauyuka, da likitocin da za su iya kula da wadanda suka kamu da cututtuka daban daban. Da hana likitoci samun ribar da ta saba ka'ida ta hanyar sayar da magani, da daidaita tsarin samar da magunguna. Sa'an nan za a yi kokarin rigakafi da shawo kan wasu manyan cututtuka, da tabbatar da ingancin abinci, da daidaita alakar dake tsakanin manufar haihuwa da sauran manufofin tattalin arziki da zaman al'umma. Haka zalika, za a yi kokarin tinkarar matsalolin da za su bullo sakamakon karuwar tsoffi a cikin al'umma, da kafa manufofi da muhallin al'umma mai kyau wanda zai iya tallafawa tsoffin mutane, da kokarin raya sana'o'i masu alaka da tsoffi.(Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku