Taron wanda shugaba Xi Jinping ya jagoranta ya samu halartar wakilan jam'iyya da wakilai na musamman da aka gayyata 2,307.
Bugu da kari, mahalarta taron sun amince da kafa tsarin sakatariyar taron da kuma ayyukan da sakatariyar taron za ta gudanar. An kuma nada Liu Yunshan a matsayin babban sakataren taron.
Tuo ya kuma shaidawa manema labarai cewa, ajandar taron sun hada da, saurara tare da nazarin rahoton da kwamitin babban taron wakilan jam'iyyar na 18 ya gabatar, da nazarin rahoton aiki da hukumar sa-ido ta kwamitin tsakiya na babban taron wakilan JKS na 18 ya gabatar, da tattauna tare da amincewa da gyaran da aka yi wa kundin tsarin jam'iyya, da zaben kwamitin tsakiya na jam'iyyar na 19 da kuma hukumar sa-ido na kwamitin jam'iyya na 19.
Gobe ne da misalin karfe 9 na safe agogon kasar Sin, ake saran za a bude babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, inda ake saran kammala taron a ranar 24 ga watan Oktoban wannan shekara.(Ibrahim)