Rahotanni sun ce, an samu jimilar ne bisa adadin da asibitoci daban-daban masu karbar wadanda harin ya rutsa da su suka bayar, inda kuma ake tsammanin yawan mutanen da suka rasa rayukansu ka iya karuwa.
A yammacin ranar Asabar da ta gabata bisa agogon kasar ne wata mota dauke da bom ta fashe a wajen wata mararrabar hanyoyi dake tsakiyar birnin Mogadishu, inda ke da yawan shaguna da otel da kuma gine-ginen gwamnati.
A daren ranar ne kuma shugaban kasar Mohammed Abdullahi Mohanmmed, ya kaddamar da zaman makoki na kwanaki 3, inda za a saukar da tutoci zuwa rabin sanda a wurare daban daban na kasar.
Zuwa yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin. Amma a cewar kafofin watsa labarun kasar, watakila kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Al-Shabaab ce ke da hannu a cikin lamarin. Kana mai yiwuwa ne, an so kai harin ga otel na Safari, inda aka fi samun yawan jami'an gwamnati da manema labaru da dai sauransu. (Bello Wang)