in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta musanta yin luguden wuta kan kungiyar Al-Shabaab a Somalia
2017-04-18 10:48:35 cri
Rundunar sojin Amurka dake aiki a Afrika (Africom) ta musanta yin luguden wuta kan kungiyar Al-Shabaab, a kudu maso yammacin Somalia a ranar Asabar da ta gabata, al'amarin da ya halaka mayakan kungiyar 100 ciki har da kwamandoji 20.

Africom da ke kai hare-hare ta sama kan kungiyar 'yan ta'adda a Somalia, ta ce tun cikin watan Junairun da ya gabata ne ta kai hari na karshe a kasar dake kahon Afrika.

A cewar Africom, Washington na aiki ne tare da kawaye da abokan huldarta a wajen samar da tsaro da kawanciyar hankali a yankuna.

Rundunar Sojin Amurka ta ce wasu gomman dakarunta kalilan, daga rundunar sojin sama na 101, za su gudanar da ayyukan tsaro da dama a Somalia, kamar yadda Gwamnatin kasar ta nema.

Wasu dakarun Amurka za su hadu da takwarorinsu na musammam dake yaki da ta'addanci a kasar, domin taimakawa sojin Somalia wajen yaki da kungiyar Al-Shabaab.

Mazauna ciki har da jami'an tsaro, sun ce a ranar Asabar, jiragen yaki sun kai hari kan maboyar mayakan Al-Shabaab a yankunan Wargaduud da El-Adde, inda wasu mayaka suka kashe sojojin Kenya a bara.

Cikin kwamdojin da harin na sanyin safiyar Asabar ya halaka, har da Abdirahman Fillow and Abdirahman Ben Dutie.

Haka zalika harin ya yi sanadin lalata wasu motocin dake shake da bama-bamai.

Amurka na da wata karamar runduna mai kunshe da dakaru 50 a Somalia, dake taimakawa da bada shawara ga dakarun kasar da na AMISOM na tarayyar Afrika wajen yaki da mayakan Al-shabaab. (Fa'iza Mustapha).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China