Wakilin musammman na shugaban Tarayyar Afrika a Somalia Francisco Madeira, ya mika nau'rar girki na tafi da gidan guda uku wanda zai iya dafawa sojoji 600 abinci.
Sauran kayayyakin sun hada da gidan sauro da hulan silke da rumfuna; wadanda za su taimakawa dakarun a sansanonin da suke.
Cikin wata sanarwa da ya fitar bayan bikin mika kayayyakin, Francisco Madeira, ya ce sun iya imanin cewa kayayyakin muhimmiyar kyauta ce daga abokiyar huldarsu wato kasar Sin, kuma za su taimaka wajen daukaka yanayin aiki na dakarun Somalia.
A nasa bangare, babban hafsan sojin kasar Mohammad Ahmad Jimaale, cewa ya yi, kayayyakin za su taimaka wajen inganta yanayin rayuwar sojoji a sansanoninsu. (Fa'iza Mustapha)