Mai Magana da yawun hukumar ta WFP Amor Almagro, ta ce, karamin jirgin saman daukar kayan yayi saukar gaggawa ne dauke da matukansa 4 wadanda babu wata matsala data same su kuma dukkansu suna cikin koshin lafiya.
Almagro ta tabbatar da cewa jirgin saman daukar kayan mai matsakaicin girma wanda hukumar WFP ta dauki shatarsa, ya gamu da matsala a lokacin da yake kokarin sauka da sanyin safiyar ranar Asabar a Garbaharey dake kudancin Somalia.
Ta kara da cewa matukan jirgin su hudu dukkanninsu babu wata matsala data samesu kuma suna cikin koshin lafiya. Sai dai a cewarta jirgin ya samu mummunar illa.
Jami'ar MDD tace, kawo yanzu ba za'a iya bayyana takamamman dalilin da ya haddasa faruwar lamarin ba, sai dai za'a gudanar da bincike na hadin gwiwa tsakanin matuka jirgin da kuma hukumomin da abin ya shafa.(Ahmad Fagam)