Jakadan Kasar Sin a Somalia Qin Jian, ya ce daliban da suka kammala karatun sakandare za su ci gaba karatu a kasar Sin, inda ake sa ran za su koma su yi amfani da iliminsu wajen gina kasarsu.
Qin Jiang ya ce tallafin wani bangare ne na kudurin kasar Sin na taimakawa wajen farfado da kasar dake kahon Afrika tare da zurfafa huldar dake tsakaninsu.
A nasa bangaren, Ministan kula da ilimin gaba da sakandare na Somalia Abdirahman Dahir Osman, ya bayyana tallafin a matsayin babban ci gaba ga taimakon da kasar Sin ke ba kasarsa, inda ya ce ya na da muhimmanci wajen kara dankon dangantaka dake tsakanin kasashen biyu. (Fa'iza Mustapha)