Fadin shagunan da aka kafa a wajen baje kolin ya kai muraba'in mita miliyan 1.185, inda aka baza nau'ikan kayayyaki fiye da dubu 160.
A bangaren da aka kebe domin nuna kayayyakin da ake fitarwa daga kasar Sin, an kafa shaguna kimanin dubu 60, wadanda ke karkashin kulawar kamfanonin kasar Sin dubu 24 da dari 4.
A bangaren kayayyakin da ake shigo da su kasar kuwa, an kafa shaguna 983 na kamfanoni 620 da suka zo daga kasashe da yankuna 33.
Taron Canton Fair wanda shi ne taron baje kolin kayayyaki mafi muhimmanci a kasar Sin, kan janyo hankalin masu sayayyar kayayyaki kimanin dubu 200 daga kasashe da yankuna fiye da 210 a ko wace shekara.
Kakakin taron na Canton Fair Xu Bin, ya furta a ranar Asabar da ta gabata cewa, yanzu yanayin tattalin arziki na da sarkakiya a ciki da wajen kasar Sin, kuma kasashen duniya na kara kokarin kare kasuwannin gida, amma duk da haka Canton Fair yana ci gaba da janyo hankalin dimbin masu sayayya daga wurare daban-daban na duniya, inda adadin mutanen ke kara karuwa a ko wace shekara.(Bello Wang)