A cikin wata sanarwa wanda mataimaki na musamman ga shugaban kasar a fannin kafafen yada labarai Femi Adesina ya fitar, shugaba Buhari ya fada cikin wasikar cewa:
"A madadin gwamnati da al'ummar Najeriya, ina farin cikin mika sakon fatan alheri da taya murna ga dukkan wakilai 2287 da kuma mambobin jam'iyyar kwamitin miliyan 89 sakamakon wannan muhimmin taro na jam'iyyar karo na 19"
"Nayi amanna cewa taron zai kasance tamkar bude wani sabon shafi ne a tarihin cigaban kasar Sin, kuma zai kasance wani gagarumin cigaba ga jam'iyyar da al'ummar Sinawa."
"Abu ne a bayyana cewa, shugabancin CPC al'amari ne da ya dace da tsarin gurguzu na al'ummar Sinawa. Kasar Sin ta samu gagarumin cigaba karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar, kuma ta kasance abar koyi ga kasashe masu tasowa har ma ga duniya baki daya. A cikin shekaru 30 da suka gabata sama da Sinawa miliyan 700 ne aka tsame su daga kangin fatara, wannan mataki ya sa kasar Sin ta kasance tamkar zakaran gwajin dafi a fadin duniya a shirin yaki da talauci."
"Karkashin kyakkyawan shugabanci na jami'yyar, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana cigaba da samar da nasarori masu yawa ga al'ummar Sinawa, kana tana kuma tabbatar da ganin mafarkin Sinawa ya tabbata na samun cigaban kasa, kasar Sin ta zama zakaran gwajin dafi a duniya. Hakika, na gamsu da irin kyakkyawar mu'amala dake tsakanin Najeriya da kasar Sin."
"Muna fatan za'a aiwatar da tsare tsare da zasu kara karfafa huldar dangantaka tsakanin kasar Sin da kasashen duniya cikin shekaru 5 masu har ma da bayansu, kuma muna fatan za'a kammala babban taron jam'iyyar karo na 19 da zabar sabon kwamitin tsakiya na jam'iyyar cikin nasara"