Bisa amanar da hukumar gudanar da al'amurran siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta damka masa, sakatare janar na kwamitin tsakiyar, Xi Jinping, ya gabatar da rahoton aiki a lokacin taron.
Sanarwar da aka bayar ta ce, an yanke kuduri cewa, za'a fara gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar karo na 19 daga ranar 18 ga watan nan na Oktoba a Beijing.
Sanarwar ta ce batutuwan da suka hada da rahoton da kwamitin tsakiya na jam'iyyar karo na 18 zai gabatar a gun babban taron wakilan jam'iyyar karo na 19, da rohoton aiki na hukumar ladabtarwa na jam'iyyar, da kuma batun gyaran fuska na kundin tsarin jam'iyyar, dukkanninsu an tattauna su kuma an amince da su a lokacin taron.
Baki daya mambobi 191 da kuma wasu karin mambobi 141 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar ne suka halarci taron.(Ahmad Fagam)