in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi tir da harin bam da aka kai Somalia
2017-10-16 09:58:34 cri

Taraayyar Afrika AU ta  yi tir da harin bam da aka kai birnin Mogadishu na Somalia da ya yi sanadin rayuka sama da 230 a ranar Asabar da ta gabata.

Shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamat, ya yi kira ga shugabancin kasar, ya kara zage damtse wajen hada kan kasar da shawo kan rarrabuwar kawuna tare da kara samar da hadin kai a dukkan matakan gwamnati.

Ya kuma bukaci al'ummomin kasashen duniya su sake daura damarar tabbatar da kai karin taimako ga hukumomin Somalia a yunkurin da suke na murkushe kungiyoyin 'yan ta'adda. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China