in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana shirye shiryen mika tsaron Somaliya ga dakarun kasar
2017-07-25 10:15:51 cri

A jiya Litinin ne aka bude wani taro na yini 4, wanda zai maida hankali ga zakulo dabarun karkata akalar harkokin tsaron Somaliya, daga ikon dakarun hadin gwiwa na tawagar AMISOM zuwa rundunar tsaron kasar.

Da yake tsokaci yayin bude taron, shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka mai lura da batun kasar ta Somaliya Caetano Madeira, ya jaddada muhimmancin samar da horo, da kayan aiki managarta ga dakarun na Somaliya, domin ba su damar rungumar namijin aikin dake gaban su.

Mr. Madeira ya ce, yanzu haka muhimmin lamari shi ne, tantance dabarun ganin dakarun na Somaliya sun samu kwarewa, ta aiwatar da kudurin maida tsaron kasar su a hannun su, domin dai cimma burin da aka sanya gaba na kawo karshen ayyukan rundunar ta AMISOM a kan lokaci.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China