in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somaliya: Dakarun rundunar AU sun kaddamar da hare-hare ta sama
2015-07-22 11:04:27 cri

Rahotanni daga kasar Somaliya na cewa, dakarun rundunar hadin gwiwa ta kungiyar AU sun kaddamar da hare-hare ta sama kan sansanonin kungiyar Al-Shabaab a garin Dinsor dake kudancin kasar.

Da yake tabbatar da hakan, magajin garin Gofgadud dake kudancin kasar Ahmed Gadid, ya shaida wa manema labaru cewa, an kaddamar da hare-haren ne da nufin kwato kauyukan dake karkashin ikon mayakan na Al-Shabaab, kafin a kai ga kwato garin na Dinsor. Kana wasu mazauna yankin sun ce, sun ga jiragen yaki na shawagi a kusa da garin na Dinsor.

Wannan mataki dai na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da kasar Uganda ta bayyana aikewa da jirage masu saukar ungulu zuwa Somaliya, don taimakawa yakin da ake yi da dakarun kungiyar ta Al-Shabaab.

A daya hannun, mataimakin babban kwamandan tawagar AMISOM mai aiki a kasar ta Somaliya Manjo Janar Mohammedesha Zeyinu, ya tabbatar wa manema labaru daukar matakan na soji, inda ya ce, dalilin hakan shi ne kakkabe mayakan Al-Shabaab daga wasu yankunan karkara da suke rike da su. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China