in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun AU sun karbi wani muhimmin yanki na kungiyar Al-Shabaab a Somaliya
2016-09-09 12:19:43 cri

Jiya Alhamis dakarun tabbatar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika (AU) dake samun goyon bayan rundunar sojojin kasar Somaliya (ANS) sun karbi wani muhimmin yanki dake kudancin Somaliya daga hannun mayakan kungiyar Al-Shabaab.

Dakarunmu na AU da na ANS sun karbi ikon mamaye yankin Abdalla Birole. Mayakan Al-Shabaab sun tsere daga yankin, kuma ba a samu mutuwa ko jikkata daga wajen mutanenmu a yayin wannan samame, in ji Joe Kibet, kakakin dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar AU dake Somaliya (AMISOM).

Yankin Abdalla Birole na kusan kilomita 60 daga yammacin kauyen Kismayo, hedkwatar mulki ta jihar Jubaland dake kudancin Somliya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China