in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta jinjinawa matakin kaddamar da majalissar dokokin Somaliya
2016-12-28 10:05:25 cri

Jagoran tawagar kungiyar AU a kasar Somaliya Francisco Madeira, ya jinjinawa nasarar da aka samu ta kaddamar da 'yan majalissun dokokin kasar Somaliya lami lafiya, yana mai cewa, hakan wata babbar nasara ce ga ci gaban dimokaradiyya a kasar.

Shugaban tawagar ta AMISOM ya kara da cewa, shan rantsuwa da wakilan al'ummar kasar suka yi a jiya Talata, wani mataki ne da ke nuna aniyar kasar Somaliya ta cimma daidaito, da warware danbarwar siyasa, da yakin basasa da kasar ta sha fama da su tsawon kusan shekaru 20.

Mr. Madeira ya kuma nuna farin cikin sa game da karin shigar al'ummar Somaliya cikin zabukan da suka gabata, adadin da ya karu da kaso mai yawa idan an kwatanta da na shekarar 2012. Har wa yau, a cewar sa, an samu karuwar wakilcin mata cikin majalissun dokokin, wanda ya kai kaso 24 bisa dari na wakilan, sabanin kaso 14 bisa dari a shekarar 2012.

Daga nan sai ya yi kira ga majalissar dokokin kasar ta 10, da ta dauki kwararar matakai, na ganin an kai ga cimma nasarar wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare da ci gaban tattalin arzikin kasa.

Jimillar 'yan majalisu 284 da suka hada da na wakilai 243, da 'yan majalisar dattijai 41 ne aka rantsar a jiyan a birnin Mogadishu cikin tsattsauran yanayi na tsaro.

Hakan dai ya kawo karshe jinkirin da a kai ta samu a baya game da kaddamar da majalissar. Ana kuma fatan nan gaba cikin wata mai zuwa, 'yan majalissar dokokin za su zabi sabon shugaban kasa.

Tun cikin watan Satumba ne dai aka yi niyar zaben sabon shugaban Somaliya, amma aka yi ta dage zaben har ya zuwa wannan lokaci.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China