Tawagar Sin ta injiniyoyi masu aikin wanzar da zaman lafiya ta tashi zuwa yankin Darfur
Tawagar Sin ta injiniyoyi masu aikin wanzar da zaman lafiya mai kunshe da jami'ai 109, ta tashi daga nan birnin Beijing na nan kasar Sin a Larabar nan, zuwa yankin Darfur dake kasar Sudan, domin fara aiki na tsawon shekara guda.
Yanzu haka dai Sin na da jami'an wanzar da zaman lafiya 2,000 dake aiki karkashin tawagogin MDD 9 a sassa daban daban na duniya, ciki hadda kasashen Sudan ta Kudu, da Mali, da Liberia, da kuma yankin Darfur na kasar Sudan.