Kasar Sin za ta kammala aikin gina tagwayen hanya a yanki mai talauci a shekarar 2020
A wajen wani dandalin kawar da talauci da aka kira a ranar 9 ga wata, mataimakin ministan harkar sufuri na kasar Sin, mista Dai Dongchang ya ce, gwamantin kasar tana kokarin gina tagwayen hanyoyi a wasu yankunan kasar dake fama da talauci, don raya tattalin arzikin wurin. Kana zuwa shekarar 2020, za a cimma burin kammala aikin gina manyan tagwayen hanyoyi a wadannan yankuna.
An ce, zuwa karshen shekarar 2016, an samu hanyoyin mota na siminti a fiye da kashi 93% na kauyukan dake yankuna masu talauci na kasar Sin.(Bello Wang)