Shugaban kasar Sin ya nanata muhimmancin shirin kawar da talauci
Ranar 17 ga watan Oktoba ita ce rana ta musamman da kasar Sin ta kebe don maida hankali kan aikin kawar da talauci. Yayin da wannan rana ke karatowa, an gudanar da wani taron jinjinawa jami'an dake kula da aikin rage talauci na kasar Sin a yau Litinin, a birnin Beijing, fadar mulkin kasar, inda shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya furta cewa, ya kamata a yi iyakacin kokari wajen gudanar da aikin kawar da talauci, duba da yadda wannan aiki yake tattare da wahala sosai. Sa'an nan shugaban ya kalubalanci dukkanin 'yan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da daukacin al'ummar kasar, da su samar da gudunmowa ga aikin rage talauci, don tabbatar da ganin an samu damar gina wata al'umma mai wadata wadda zata rayu cikin walwala.(Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku