in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sana'ar kai kayayyakin da aka saya gida a kasar Sin ta ba da babbar gudummawa ga ci gaban sana'ar a duk duniya
2017-10-09 13:17:20 cri
Yau Litinin 9 ga wata, rana ce ta aikewa da sako ta duniya karo na 48 wato World Post Day, wadda aka ware musammam domin inganta hanyoyin aikewa da sakonni. Shugaban hukumar kula da harkokin aikewa da sako ta kasar Sin, Mista Ma Junshen ya bayyana cewa, cikin shekaru biyar da suka gabata, sana'ar aikewa da sako na bunkasa cikin sauri a kasar, musamman sana'ar kai kayayyakin da aka saya gida. Wannan sana'a, wato kai kayayyakin da aka saya gida a kasar Sin, ta zama ta farko a duk fadin duniya cikin jerin shekaru ukun da suka wuce, kana, yawan gudummawar da ta bayar ga habakar sana'ar a duniya ya kai kashi 40 bisa dari.

Har wa yau, Mista Ma ya ce, cikin shekarun biyar da suka gabata, yawan sana'ar aikewa da sako ta kasar Sin ya ninka kusan sau hudu, kana, adadin kudin da aka samu daga sana'ar ya ninka har sau 3. A halin yanzu, babban kamfanin aikewa da sako na kasar Sin wato China Post Group Corporation, yana cikin manyan kamfanonin aikewa da sako guda uku, wadanda suke kan gaba a duk fadin duniya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China