Bisa wannan rahoton da hukumomin kasar suka gabatar, an ce yawan kudin da kasar Sin ta ware domin raya kimiyya da fasaha ya kai matsayin yawan kudin da wata kasar dake da ci gaban tattalin arziki ke zubawa wannan fanni. Ga misali, an ce yadda kasar Sin take kokarin raya sabuwar kimiyya ya riga ya zarce wani matsakaicin matsayi tsakanin kasashe 15 mambobin kungiyar kasashen Turai EU, sai dai bai kai wasu kasashen da suka mai da hankali matuka kan kirkiro sabbin fasahohi ba, irinsu Isra'ila, Koriya ta Kudu, da Japan.(Bello Wang)