in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake rantsar da Ali Bongo Ondimba a matsayin shugaban Gabon
2016-09-28 10:43:44 cri

Shugaban Gabon Ali Bongo Ondimba ya yi rantsuwar kama aiki na wa'adi na biyu na shekaru bakwai masu zuwa a ranar Talata, kwanaki hudu bayan kotun tsarin mulkin kasar ta amince da sake samun nasararsa cikin babban zabe, a cewar fadar shugaban kasar.

Ali Bongo ya yi rantsuwar kama aiki a ranar Talata a birnin Libreville a gaban idon shugabannin kasashen Afrika hudu. "Na rantse wajen kiyaye dukkan karfina domin moriyar al'ummar Gabon, a kokarin tabbatar da jin dadinsu da kuma kare su daga duk wata matsala, da girmama da kare kundin tsarin mulki da kasa mai 'yanci, da cika nauyin dake bisa wuyana yadda ya kamata da kuma kasancewa mai adalci ga kowa," in ji shugaban, hannun hagu kan kundin tsarin mulki, kana hannun dama gaban tutar kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China